Tuesday, 10 October 2017

Aisha Buhari tayI magana mai kyau gameda gwamnatin buhariIdan har shugaban kasa zai iya yin watanni a Kasar waje sabo da rashin kayan aiki a asibitin dake fadan sa, ina talakawan da basa da galihu zasu sa kan su a Nigeria ???


Hajiya Aisha Buhari ta sake kwanto kura a taron masu ruwa da tsaki na wata hukumar kula da lafiyar mata da yara, wanda aka gudanar a asibitin da ke cikin fadar shugaban kasar, inda take cewa:

"Na ji matukar dadi da nake wannan maganar a lokacin da shugaban asibitin fadar Dr. Hussain Munir yake nan, kowa ya san cewa wata shida da suka gabata mijina ba shi da isasshiyar lafiya, amma yanzu mun gode Allah ya samu sauki."

"Makonni kadan da suka gabata, na yi fama da rashin lafiya, sai likitocin asibitin fadar shugaban kasa suka shawarce ni cewa na hau jirgin farko zuwa London, amma sai na ki."
"Na ce musu dole ne a duba ni a gida Najeriya, saboda akwai kudin da aka ware musamman don kula da asibitin," in ji ta.

Hajiya Aisha ta kara da cewa: "Idan dai har shugaban kasa zai shafe watanni da dama a wani asibiti a kasar waje, to za a yi mamakin halin da talakan kasar kuma ke ciki wanda ba shi da gata."

"To idan har kudin da aka ware don kula da sibitin ya kai miliyan 100, za mu so mu san ta yaya aka kashe kudin.

Rannan da nasa a tambaya ko suna da injin daukar hoton kashi sai suka ce ba ya aiki, ba su san cewa ni ce nake son zuwa a duba ni ba."

Uwargidan shugaban kasar ta kara da cewa hakan ne ya sa ta tafi wani asibitin kudi mallakin 'yan kasar waje don a duba ta.
"Na ce musu dole ne a duba ni a gida Najeriya, saboda akwai kudin da aka ware musamman don kula da asibitin,"

"Idan har abu irin wannan zai faru da ni, to lallai ba na bukatar tambayar matan gwamnoni abin da ke faruwa a jihohinsu. Nan Abuja ce inda fadar shugaban kasa take.

"Duk da cewa na ji wani a jawabinsa ya ce Najeriya daga cikin kasashen da take da tsari mai kyau, lallai na yarda, amma matsalarmu ita ce jajircewa don ganin an aiwatar da abu."

kasafin kudin da aka ware na 2017 ga asibitin fadar shugaban kasa dai, wanda kuma majalisar dattawa ta amince da shi ya fi naira miliyan 330,000.


Ku kasance da hausa7............


EmoticonEmoticon