Saturday, 7 October 2017

Almijiri Yayi kokarin kashe Malaminsa

TagsAlmajiri Ya Yi Yunkurin Halaka Malaminsa Da Fiya-Fiya A Keffi.
Ashiru Abdulqadir Lamarin Ya faru ne ranar Juma'ar da ta gabata a unguwar Rimi da ke garin Keffi a jihar Nasarawa, inda matashin almajirin mai suna Muhammadu Sani dan shekaru 16 a duniya ya yi kokarin halaka dattijon malaminsa, Malam Aliyu Baba Akawu.

Wata majiya da ta nemi a sakaye sunanta ta bayyana mana cewa Malam Aliyu ya aika ansayo masa kokon karyawa kamar yadda ya saba karyawa a wani zaure da ke gidansa amma bai kai ga sha ba sai almajirin ya shigo zauren kamar wanda zai dauki kur'ani shi kuma malamin bai ankara ba saboda kasancewar yana da lalurar ido ba ya gani sosai sai almajirin ya yi amfani da wannan damar ya zuba fiya fiya a cikin kunun malam sannan ya mayar ya rufe.

Ko da malam ya zo zai karya, ya dauki kununsa zai sha da zuciya daya, ya yi kurba daya, ya sake yin ta biyu sai ya ji dandanon kunun ya canza ba kamar yadda ya saba ji ba ga kuma wani warin da bai aminta da shi ba, sai malam ya yi kiran 'yarsa Jimmai bayan ta zo sai ya ce ta duba masa meye a cikin kokonsa sai aka ce ai fiya-fiya aka sa a ciki.

Sai aka fara bincike akan waye ya shiga zauren malam har aka gano cewa Muhammadu Sani ne ya shiga da aka tambaye shi mai ya sa ya sa fiya-fiya a cikin kunun malam sai ya ce saboda ba ya son karatu ne shi ya sa ya ke son malam ya mutu don ya koma wajen iyayensa.

Shi kuma malam aka ba shi madarar ruwa da manja saboda abun bai yi tsanani ba, sannan aka kira iyayen almajirin a waya suka zo aka sasanta lamarin a gida suka dauki yaronsu suka tafi da shi.

Madogara: Leadership Hausa.


EmoticonEmoticon