Saturday, 7 October 2017

Anmanta Almakashi a cikinsa Har tsawon shekara 18

TagsLikitoci a kasar Vietnam sun yi sa'ar cire almakashi 2 da aka manta a cikin wani mutum shekaru 18 da suka gabata.Mutumin wanda wani mazaunin babban birnin kasar Vietnam Hanoi ne, ya ci gaba da rayuwarsa tare da almakasai 2 masu tsawon sentimita 15 kowanne, tun bayan wata tiyata da aka yi masa, sabili da hatsarin mota da ya yi a shekaru 18 da suka shude.

An gano wadannan almakasan a lokacin da mutumin ya je asibiti domin a duba lafiyar cikinsa wanda yake jajen cewa yana ciwo, ba tare da ya san musabbabin hakan ba.

Likitoci sun yi nasarar cire wadannan almakasan daga cikin majinyacin mai shekaru 54 da haifuwa, ba tare da wata matsala ba.

Ku kasance da Hausa7.tk


EmoticonEmoticon