Tuesday, 3 October 2017

Dalilin da yasa za'a yafema dangote haraji

- Za su yi wa gwamnatin Najeriya tituna a kan bashi

- Sai su ciri kudin aikin a cikin harajin da zasu na biya

- Ana jita-jita cewa yafiyar shekara 10 za'a musu, amma dangote group ta musanta 

Hukumar zartarwa ta Gidauniyar Dangote ta ce za'a a yafe musu biyan haraji har na shekara uku in sun yi aikin titin Apapa zuwa Oworonshoki, wanda tsawon hanyar ya kai kilomita 35. Devakuma Edwin, babban darekta a gidauniyar, ne ya fadi haka.

Ya ce, "Kamfanin mu bai taba ribatuwa da yafiyar haraji ba sai dai in na gaba daya ma'ikatu aka yi. Ana jita-jita cewa na shekara 10 za'a yafe mana, ba haka bane.

"Gwamnati bata da kudi a hannu, shi ya sa ta bude ga ko wanne kamfani zai iya kawo jadawalin a nawa zai iya yin aikin titin a kan bashi. Mu da muka kai namu sai aka zabe mu mu yi saboda kudin mu yayi kasa da na kowa. Saboda haka gwamnati ta zabe mu da mu yi aikin. Mu kuma muka ce mata zamu cirai kudin a cikin harajin da zamu na biya har na shekara uku."

Gwamnati ta ce aikin titin ya kunshi titunan Creek da Liverpool, Marine Beach zuwa mil 2, Oshodi, Oworonshoki zuwa karshen tol-get a kan babban titin zuwa Ibadan.


EmoticonEmoticon