Monday, 2 October 2017

Dalilin da yasa zanyi takara da buhari : fasto Bakare


Fasto Tunde Bakare, ya bada dalilai da ya sa ya tsaya a matsayin abokin takaran shugaba Buhari
- Faston yace ya yarda da tsayawa a madadin abokin takaran Buhari ne saboda ra’ayin Buhari kan sake gina Najeriya- Ya ce kudirin Buhari ya sa shi samu goyon bayan yan Najeriya masu kyakkyawan manufa don zama shugaban kasaBabban limamin cocin Latter Rain Assembly, Fasto Tunde Bakare, ya bada dalilai da ya sa ya tsaya a matsayin abokin takaran Muhammadu Buhari a karkashin jam’iyyar Congress for Progressive Change, (CPC).
Ya bayyana haka ne a lokacin da jawabi kan ranar bikin samun yanci a harabar hedikwatan cocin shi dake Legas.
Dalilin da yasa na amince da tsayawa takara tare da Buhari – Fasto Tunde Bakare
A jawabin sa, faston yace ya yarda da tsayawa a madadin abokin takaran Buhari ne saboda ra’ayin Buhari kan sake gina Najeriya, wanda a cewar shi, abu ne na kwarai.

Ya kara da cewa a bisa wannan dalilin ne, Buhari ya samu goyon bayan yan Najeriya masu kyakkyawan manufa don zama shugaban kasa.
A baya  hausa7 ta rahoto cewa Wata kungiya ta yabi ziyara da shugaba Muhammadu Buhari ya kai wa Rondunar soji dake yaki da ta’addanci a Maiduguri, jihar Borno.
Kungiyar, mai suna Coalition Against Terrorism and Extremism (CATE) ta yabi shugaban ne da shuwagabannin tsaro kan amfani da ranar bikin yancin kai wajen ziyartan rundunan dake yanki da ta'aciddan arewa maso gabas.
Kungiyar CATE tace ziyara da shugaban ya kai ba zai kasance taimako ga rundunan ba wajen yaki da ta’addanci kawai amma zai kara wa rundunar kuzari.


EmoticonEmoticon