Saturday, 7 October 2017

Donald trump: Iran da Koriya ta arewa sai sunyi nadama


A yayin wani taron manema labarai da shugaban Amurka da wasu manyan kwamnadojin sojin kasarsa suka gudanar, Donald Trump ya ce kasashen Iran da Koriya ta Arewa sai sun yi nadama.


A yayin wani taron manema labarai da shugaban Amurka da wasu manyan kwamnadojin sojin kasarsa suka gudanar, Donald Trump ya ce kasashen Iran da Koriya ta Arewa sai sun yi nadama.

Kafafan yada labaran duniya sun yi wa wannan furucin da Trump ya yi, a yayin da yake tsakar daukar hoto da manyan sojojin Amurka, tamkar wani shiru gabanin afkawar mahaukaciyar guguwa.

Amma ya tashi mayar wa 'yan jarida martani, sai shugaban na kasar Amurka ya ce :"Mahaukaciyar guguwa fa? Iran ko kuma Koriya ? Wacce ce ma ta isa ta yi mana wani abu ? Ku bar yawan kwankwanto. Koma mene ne zaku gani, haka zalika Iran da Koriya ta Arewa ma za su gani".


Manema labarai sun yi namijin kokari a wajen gano mana'anar wannan kalamin da Trump ya yi, game da Koriya ta Arewa da kuma Iran, amma hakarsu bata cimma ruwa ba.Domin shugaban na Amurka ya ki bada kai bori ya hau.

An tabbatar da cewa, matakin da Donald Trump ya dauka a baya baya nan, wanda kuma gidajen jaridun Amurka suka kira da suna "Shiru gabanin afkwar mahaukaciyar guguwa" ko kuma "Dunkulalliyar Barazana" ita ce barazana mafi muni da aka taba yi wa Koriya ta Arewa da Iran.

A gefe daya kuma, sabon matakin da Trump ke gaf dauka a wajen yin wancakali da yarjejeniyar nukiliya da wasu manyan kasashen yamma 5 suka yi da Iran,zai iya kara jefa kasar Farisawa a cikin mawuyacin hali.

Trump dai ya jima yana Allah wadai da wannan yarjejeniyar, tun a lokacin farfagandar zaben shugabancin kasar Amurka,inda ya kira ta da suna "Abu mafi muni da aka taba yi a tarihin kasashen yamma".

Game da batun Koriya ta Arewa kuma, a yayin da ya halarci babban taron majalisar dinkin duniya karo na 72,Trump ya dauki alkawarin gushe ta daga taswirar duniya.Ku kasance da Hausa7.tk


EmoticonEmoticon