Wednesday, 4 October 2017

Hotuna motoci masu tashi sama da akayisu domin taxi
An fara gwajin motocin tasi marasa matuka wadanda za su rika tashi sama a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).
Motar wadda za ta rika daukar fasinja biyu, ta yi tafiyar minti 15 ne yayin gwajin farko a makon jiya

Wani kamfanin Volocopter na kasar Jamus wanda yake kera jirage marasa matuka ne ya kera tasin

Motar wadda take amfani da wutar lantarki, za ta rika tafiyar minti 30 ne kawai, bisa gudun kilomita 25 a tsawon minti 30

An fara gwada tasin ne a Jamus a watan Afrilun bana
An yi gwajin tasin ne a unguwar Jumeirah ta gabar teku kuma za a fara amfani da su ne nan da shekara biyar masu zuwa.


EmoticonEmoticon