Monday, 9 October 2017

Yadda zaku kera na'urar Kyankyansar kwai
MASU SHA'AWAN HADA NA'URAN KYANKYASAN KOYIN KAZA(HEN).Yau nazo mana da bayani gamedayadda zaka hada na,uran kyankyasan kwan kaza wanda akafi sani dasuna incubator wanda yake amfani da wutan lantarki. Daga farko maikaratu ya karanta bayani na anitse domin yafahimci yadda bayanin yake.

1. Daga farko anaso kasami gidan da zaka hada na na,uran, idan kaga dama zaka sami empty na kwalin Tv ko kwalin karamin fridge hakan nan, ko kuma wani gidan katako idan zaka iya hadawa saika hadagidan katakon yayi kama da tsarinsquare box wato kaman yadda kagani a hoton nan.

2. Ana so kasami kasami koyin wuta kasa aciki, amma karkayi amfanida irin fararen koyin wutan flaurecense fa. Kasayi normal jan koyi 60watt inaga daifi tinda na pratical ne.
3. Bayan kasa koyi kamar yadda kagani a hotona to saika zuba koyin ka aciki, yadanganta da yawan koyin ka, idan space din dake cikin sa zai dauki koyi goma ko 8 to saikasa koyayen amma karsuyi yawa.

4. Kanemo dan karamin kofi ko kwano saika zuba ruwa saikasaka kwanon ruwan acikin incubator dinka kasa ata gefen wajen da kazuba koyinka kamar yadda kagani a hoton nan

5. Kasayi digital thermometer Akasuwa inaga baifi 500 ba, shi amfanin sa yana nuna yanayin tempreture din ne, to saika saka thermometer dinka, ba,aso zafin cikin incubator din yayi kasada 97, karkuma yahaura 101, duk dakansa thermometer din zai nuna maka yana dan karamin screen haka.

6. Daga karshe, anaso kullum da safe kajujjuya koyin, da ranama haka, da daddare ma haka, zuwa na tsawon kwana 18 to daga lokacin kadena juyawa. Yana cikawa kwana 21 kajira kaga ikon Allah, domin insha Allahu zasu kinkishe.


Ku kasance da hausa7..........


EmoticonEmoticon