Saturday, 7 October 2017

Matashi yakashe abokinsa kan bacewar saniya

TagsWani matashi mai suna Umar Muhammad dan kimanin shekara 23 ya kashe abokinsa mai suna Mustafa Muhammad mai kimanin shekara 22 a kan bacewar wata saniya.
Ana zargin Umar ya kashe abokinsa ne lokacin da yake kwance a karkashin wata itaciya a karamar Hukumar Kalgo da ke Jihar Kebbi.


dan uwan marigayin wanda ya yi magana da Aminiya, ya ce Mustafa da Umar abokan juna ne na tsawon shekara shida. Ya ce Mustapha ne ya gayyaci wanda ake tuhuma don taimakawa wajen kula da shanun da aka ba shi.


Ya ce lokacin da marigayin ya lura cewa daya daga cikin shanu da ke cikin garken ta bata sai tambayi Umar wanda ya kasa bayar da gamsasshen bayani kan bacewar saniyar, inda marigayin ya ce zai sanar da mai shanun.


dan uwan marigayin ya kara da cewa, wanda ake tuhumar da marigayin sun fita ranar Juma’ar makon jiya zuwa inda suke hutawa, inda wanda ake zargin ya yi amfani da gatarin da ke hannunsa wajen sare Mustafa a yayin da yake hutawa a kasan wata itaciya. Daga nan sai Umar din ya dawo gida ya yi wanka, amma da suka tambaye shi game da Mustafa sai ya ce ya bar shi a daji.


Ya ce daga nan ne aka fita neman Mustafa, inda aka gano gawarsa inda ya kashe shi bayan kwana biyu da kashe shi.


Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kebbi DSP Mustafa Sulaiman ya shaida wa wakilinmu cewa, wanda ake zargin mai suna Umar Muhammad yana hannun ’yan sanda kuma sun fara gudanar da bincike a kan tuhumar kisan da ake yi masa.Ku kasance da hausa7.tk akoda yaushe..........


EmoticonEmoticon