Sunday, 8 October 2017

Patience jonathan: yakamata Shugaban kasa BuharI Ya dunga mutunta niA ranar Litinin din da ta gabata ne Uwargidar tsohon shugaban Najeriya, Madam Patience Jonathan ta fitar da wata sanarwa, inda ta bukaci Shugaba Muhammadu Buhari da ya rika mutunta ta kamar yadda mai gidanta ke mutunta A’isha Buhari bayan kayen da suka sha a zaben 2011. Sannan kuma ta koka kan yadda hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta sako ta a gaba bisa zargin al’mundahana.

Uwargidar tsohon shugaban kasan, ta kara da cewa, abin da ya faru a lokacin yakin neman zaben 2015 wadda ya kawo karshen mulkin mijin nata, bai kamata ya zama silar musguna ma ta ba a yanzu.

Har ila yau, Patience Jonathan ta bukaci Shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ya ja kunnen mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu da ta ce manufarsa kawai ita ce ya ga bayan iyalinta baki daya.

Sannan ta kara da cewa, “Ya kamata Buhari ya dauki darasi daga salon mulkin shugaban Amurka, Donald Trump, wanda bai damu da sha’anin uwargidan Barack Obama ba, bayan ya karbi mulki daga hannunsu,” a cewarta.

Madam Jonathan ta ce, Hukumar EFCC na binciken ta ne saboda rawar da ta taka a lokacin shirye-shiryen zaben 2015 da ya kawo karshen mulkin nasu a karkashin jam’iyyar PDP. Koda yake cikin munanan kalaman da ta yi gabanin gudanar da zaben, ta bayyana Shugaba Buhari a matsayin mutum mai raunin kwakwaluwa.


Ku kasance da hausa7.tk a koda yaushe..............


EmoticonEmoticon