Tuesday, 3 October 2017

Wasu Yan kungiyar asiri sun kasheKimanin mutum biyar suka mutu a sakamakon fada tsakanin matasa ’yan kungiyar asiri ta bikings da kuma ta Skylow a Kalaba Jihar Kurosriba a Talatar da ta gabata.kungiyoyin biyu suna rikakkar gaba a tsakaninsu, wanda haka ya haddasa matsalar rashin kwanciyar hankali saboda yawan fadace-fadacen ’yan kungiyar asiri da ya fi kamari a karamar Hukumar Kalaba ta Kudu, duk kuwa da irin matakan tsaro da rundunar ’yan sandan jihar ke bayarwa.

Cikin wadanda aka kashe har da wani dan takarar mukamin Kansila a mazaba ta 8 da ke karamar Hukumar Kalaba ta Kudu ya gamu da ajalinsa a huce haushi da ’yan kungiyar asiri ta Skylow ta kaddamar. Haka ma wani mai suna Mesembe, wanda shi ma dan kungiyar asirin ne, ya gamu da ajalinsa a kwanton bauna da ’yan kungiyar na Skylow suka yi masa a Layin Eyo Ita, a wani samame da suka kawo daga Layin Edibe-Edibe, kamar yadda dama kungiyoyin asirin suka sha kai wa juna hare-haren sari-ka-noke.

Wata majiya a yankin da abin ya faru ta shaida wa Aminiya cewa, tun kimanin kwanaki uku da suka gabata, kungiyoyin Scorpion da Skylow aka gan su suna kulla yadda za su kai wa ’yan kungiyar bikings farmakin, a Layin Mayne Abenue da Ekpo Abasi saboda kashe musu wani jigo a kungiyar tasu mai suna Ecomoc da suka yi zargin daya kungiyar ta yi.

Aminiya ta tuntubi Kakakin rundunar ’yan sandan Kurosriba, Irene Ugbo game da lamarin, inda ta tabbatar da faruwar fadan; sai dai ta ce mutum daya aka kashe a artabun.

Source: aminiya


EmoticonEmoticon