- Fadar Shugaban Kasa ta bayyana dalili da har ta kai ga Buhari zuwa kasan waje domin duba lafiyar sa

- Femi Adesina ya ce daman Shugaba Buhari bai yi alkawarin kin fita waje don neman magani ba

- Sai dai ma daura laifin rashin kayan aiki da ya yi a kan Gwamnatin da ta gabata.

Fadar Shugaban Kasa, ta bakin Femi Adesina wanda shi mai magana da yawun Shugaban Kasa, ya ce daman Buhari bai yi alkawarin cewa ba zai je kasar waje domin duba lafiyar sa ba idan a ka zabe shi a 2015.

Adesina ya yi wannan jawabi ne yayin da je gidan talabijin din AIT domin wani shiri na su.


Mai magana da yawun Jam'iyyar APC na kasa, Bolaji Abdullahi wadda akayi hira dashi tare da Femi Adesina yace zancen da akeyi cewa shugaba Buhari yayi alkawarin bazai tafi kasashen ketare neman magani ba, ba gaskiya bane.

Adesina ya kara jadada maganar Abdullahi inda yace shugaba Buhari bai san da wannan zancen ba, balle ma ya amince dashi.

Adesina ya kara da cewa hasali ma rashin ingancin asibitocin Najeriya sakamakon rashin kullawa da gwamnatocin PDP da suka shude sukayi ne babban dalilin da yasa shugaba Buhari yake tafiya kasashen waje.


©Hausa7.ML

Post a Comment

 
Top